Sirrin rike miji
Sirrin rike miji
June 20, 2025 at 02:13 PM
KISSA NA 1: Bilal (RA) da Kaunar Annabi Muhammad (SAW) Bilal (RA), bawan Habasha ne da aka yi masa azaba mai tsanani saboda ya karɓi Musulunci. Ubangidansa Umayya ibn Khalaf yana sa shi a kwance a ƙasa mai zafi, yana ɗora dutse mai nauyi a kansa, yana ce masa ya bar Musulunci. Amma Bilal bai faɗi komai ba sai: “Ahad! Ahad!” (Wato: Allah ɗaya ne! Allah ɗaya ne!) Daga baya, lokacin da Musulmi suka ƙwace Makka, Abu Bakr (RA) ya sayi Bilal daga bauta ya 'yantar da shi. Bilal ya zama mu’azzinin farko a tarihin Musulunci. Amma lokacin da Annabi Muhammad (SAW) ya rasu, Bilal ya daina yin azan saboda bakin ciki. Duk lokacin da ya zo wajen “Ash-hadu anna Muhammadan Rasulullah” sai ya fashe da kuka. Bilal ya ce: “Bazan iya sake cewa sunan Annabi ba, bayan da ya bar duniya.” Guzuri Domin Makoma ✍️
❤️ 👍 😢 🙏 😮 20

Comments