Sirrin rike miji
Sirrin rike miji
June 20, 2025 at 02:20 PM
KU BADA FIFIKO WAJEN ANFANI DA WADANNAN KAYAN MARMARI. BARKAN MU DA SAFIYA SANADARAN Gina jiki na daga cikin tubali ko ginshikin wanzuwar jikin Dan Adam. Akwai mafi Yawan wadannan sanadarai da jikin mu ke samarwa, mafi Yawan wasu mukan samesu ta hanyar Abinci da Kuma ainahin magungunan su Kai tsaye. Karancin ko rashin ire iren wadannan sanadarai Matsala ne, hakan kanjayo wasu Matsalolin rayuwa. Na fito da misalan wadannan sanadarai da irin Matsalar da rashin kowanne AJIKI zai haifar. Vitamin B1: shine Thiamin, rashin sa ajiki na haddasa matsala ta Zuciya, Beriberi da Kuma kwakwalwa. Vitamin B2: Shine Riboflavin, Rasa ko karancinsa a jiki na haddasa Matsala ta baki da Kuma Fata. Vitamin B3: Shine Niacin, Rasa wannan sanadarin Yana sa Matsalolin Fata, vagina, Dubura, Baki da Kuma Kwakwalwa. Vitamin B6: Shine Pyridoxine, Rashin da na haddasa Matsalolin fata, Baki, Tashin Zuciya da Amai, Rashin Jini, juwa da rashin karfin jiki. Folate (folic acid): Rashin Folic acid ajiki na haddasa rashin Jini Kai tsaye. Vitamin B12: Rashin Wannan mahimmin sanadari na haddasa Rashin Jini. Vitamin C: Wato Ascorbic acid, Rashin Wannan sanadari Yana sa a hadu da matsala ta scurvy, fragile capillaries, Rashin Warkewar Gyambo ko ciwo da wuri da Kuma bone deformity ga yara. Vitamin D: Rashin sa Wanda kusan Babu wasu kayan Abinci da za a ko ake samu da sauki wadanda suka kunshi wannan sanadari, jikimmu na anfani da hasken Rana wajen Samar dashi. Rashin sa Yana sa Cutukan Kashi, bone Deformity da Kuma (rickets) ga yara. Vitamin E: Rashin sa ajiki na kawo anemia. Vitamin K: Rashin Vitamin K musamman ga Mata na haddasa abnormal bleeding. Sai a kula. ✍️ Kabir Yusuf Danwurin Dutsi
👍 🙏 5

Comments