Sirrin rike miji
Sirrin rike miji
June 20, 2025 at 02:22 PM
FALALAR SALLAR JAM'I (SALLAH A CIKIN JAMA'A) Sallar jam'i tana da mahimmanci sosai har wasu daga cikin malamai sun ce wajibi ce, idan mutum baya zuwa sallar jam'i yayi babban saɓo, wasu sun ce sunna ce mai ƙarfi, wanda baya zuwa sallar jam'i yayi babbar asara, wasu daga cikin Malaman sun tafi tafi akan sharaɗi ce ta karɓar sallah.idan mutum baya zuwa sallar jam'i da gangan sallar sa ta ɓaci. Akwai hujjoji a cikin Alkur'ani mai girma da hadisan Annabi saw, da suke tabbatar da mahimmanci salla a cikin jama'a, Allah ta'ala yace kuyi Ruku'u tare da masu yin ruku'u, (wato kuyi salla tare da masu yin salla,) An ruwaito daga Abdullahi ƊAN Umar RA yace :Manzon Allah saw yace :Salla cikin Jam'i tafi mutum yayi salla shi kaɗai da daraja 25, Buhari 645 da Muslum 650, Hadisi ya tabbata daga Abu Hurairah RA Mutum yayi salla a cikin jam'i yafi yayi salla shi kaɗai a cikin gidansa ko yayi salla a kasuwar sa, da da daraja 27, Bukhari 477, Muslum 649. Daga Abu Saidul khudriy yace Manzon Allah saw yace, Sallar jam'i ta fifici sallar mutum shi kaɗai da darajoji 25.. Bukhari 646. Daga Usman Ɗan Affan RA yace :Manzon Allah saw yace : Duk wanda yayi sallar insha a cikin jam'i kamar tsayuwar rabin dare yana salla, wanda yayi sallar asuba a cikin jam'i, kamar ya yi tsayuwar dare dukkan sa yana salla. Muslim ya ruwaito 656. Daga Sayyadina Usman Ɗan Affan RA yace Manzon Allah saw yace : Duk wanda yayi alwala ya kyautata alwalar sa, sannan ya tafi zuwa masallaci, yayi salla a cikin jam'i, tare da jama'a, to Allah zai gafarta masa zunuban sa. Muslim ya ruwaito 232. Waɗannan hadisai sun ƙara tabbatar mana da mahimmanci salla a cikin jam'i da kuma falalar da ake samu. HIKMAR YIN SALLA A CIKIN JAM'I Bayan kasancewar salla a cikin jam'i tana da mahimmanci da falala, kuma akwai hikmomi da fa'idoji masu yawa da malamai suka lura zaa samu idan ana yin salla tare a cikin jam'i. 1 Yin sallah a cikin jam'i yana kawo soyayya tsakanin al'umma, saboda yawan haɗuwa da ake yi ana salla tare kowa zai san ɗan uwansa, 2 Yin salla a cikin jam'i yana kawo haɗin kai tsakanin musulmi, da sanin halin da maƙoci yake ciki, 3 Yin salla a cikin jam'i yana koyawa mutane tsari, da shugabanci, da biyayya, domin duk yawan masallacin nan suna koyi da liman guda ɗayan ne. 4. Yin salla a cikin jam'i yana bayyana ƙarin musulmi, da izza, ta musulunci 5. Yin salla a cikin jam'i yana koyawa musulmi hakuri da juriya, wajan zuwa salla kullum sai biyar babu gazawa,. 6 Yin salla a cikin jam'i yana koya mana sanin halin da wasu musulmi suke ciki, kamar talakawa da marayu da marasa lafiya, idan aka ga kwana biyu mutum baya zuwa sai a bincika, domin ko yana buƙatar kawo ɗauki. 7 Yin salla cikin jam'i yana ƙara himma da ƙwazo wajan ibada, da cire kasala, da nawa,. 8 Yin salla a cikin jam'i yana cirewa mutum girman kai, domin zai ga a masallaci kowa ɗaya ne babu bambanci. Tsakanin talaka da mai kuɗi ko babba da yaro, ko malami da jahili, ko mai mulki da talaka,. Duk ɗaya suke a gaban Allah, wanda yafi shine wanda yafi tsoran Allah. 9 Yin Salla a cikin jam'i tare da yara, yana kara masu tabbatuwa akan addini ko bayan wacewar iyayan su, saboda zasu saba da salla, kuma tarbiyyar su zata gyaru. 10 Yin sallah a cikin jam'i yana jawo ƙarin ilmi da wayewa saboda yawan karatu da darussa da ake gabatarwa a masallaci. Musamman bayan asuba da bayan magrib. Ya al'ummar musulmi mu kula sosai da zuwa salla cikin jam'i, kada mu bari sheɗan ya rinjaye mu, ya hana mu wannan babban alkhairi da yake kore munafinci daga zuwa zuciya da aiki, domin munafukai basa zuwa sallar jam'i, da sunji an kira salla sai, jikin su ya mutu, kasala da nauyin jiki ya lullaɓai su. Allah ya tsare mana imanin su ya sa mu dinƙa kula da salla a cikin jam'i. Akwai salloli da ake yi musu jam'i bayan salloli biyar, sune sallar tarawihi ko asham, da sallar kusufun wata da sallar kusufin rana, da sallar idi guda biyu, Akwai kuma salloli guda shida da baa yi musu jam'i, sune sallar duha (walaha) sallar gaisuwar masallaci, (tahiyyatul Masjid) rakaar ɗawafi ( sallar da ake yi bayan an gama ɗawafi kowa zaiyi tasa shi kaɗai ba'a yi mata jam'i) sallar nafila da ake yi bayan an gama alwala, sallar istikhara, (sallar neman zaɓi daga wajan Allah) sallar tuba (idan mutum ya yi laifi yayi nadama yana so Allah ya yafe masa sai yayi salla rakaa biyu ya nemi gafara), salatus tasbihi , waɗannan salloli da muka lissafa guda shiga ba'a yin su a cikin jam'i, kowa zai yi tasa shi kaɗai. UZRIN DA ZAA IYA FASA ZUWA SALLAR JAM'I SABODA SHI, Akwai wasu abubuwa da idan sun taso zaa iya fasa zuwa sallar jam'i saboda su, kamar ruwan sama mai tsanani, da santsi da taɓo mai tsanani, da sanyi mai tsanani, waɗanda suka iya jawo cutawa, ga jama'a, ana iya barin salla a masallaci, kowa yayi sallar sa a gida. Ko kuma uzri na rashin lafiya ko idan ana cikin halin tsoro da tashin hankali, ko kuma mutum yana tsananin matsuwa da kashi ko fitsari ko yunwa mai tsanani, ko yaci albasa ko tafarnuwa, ko lawashi, dukkan wannan yana iya zama uzri, na barin zuwa jam'i, idan ba mayar da shi al'ada aka yi ba. SIFFOFIN LIMAN. Manzon Allah saw yayi limanci kuma ya naɗa limamai kuma ya faɗi yadda ya kamata limamai su kasance, ya kuma bayyana cewa, Wanda zai yi wa mutane limanci ya zama yana da ilmin Alkurnani mai girma, ya iya karayu sosai ya kwarai wajan sarrafa Karatun Alkurnani mai girma da sanin ƙa’idojin sa, kuma yasan fassara kuma yana aiki da shi, idan ansami mutum biyu, duk sunsan Alkurnani, sai a duba wanda yafi kwarewa, idan duk suna da kwarewa sai a duba wa yafi sanin Sunnah ta Annabi, saw, wajan ilmi da aiki,idan sun zama duk masana sunna sai a duba wa yafi, idan ba'a sami wanda yafi ba, sai a duba sauran fannoni, kamar Hijra da daɗewa a musulunci ko shekaru, ko asali ko tsafta da kyawun kama da kamala da tsantseni da gudun duniya, da makamantansu. MAHIMMANCI ZUWA MASALLACI DA WURI DA SAMUN SAWUN GABA. Ya kamata mu dinga zuwa masallaci da wuri domin samun falala da daraja, da samun sahun farko, Manzon Allah saw yace :Da mutane sun san abinda ake samu na lada a cikin kiran salla da samun sahun farko, da sunyi kuri'a a kai, saboda yawan masu buƙata. Manzon Allah saw yace :Wanda yayi salla kwana arba'in a cikin jam'i baya rasa Kabbarar harama, Allah zai rubuta masa, kuɓuta daga abubuwa biyu na ɗaya ba zai shiga wuta ba, na biyu zaa raba shi da munafinci, Sahihu Timiziy 200. Wajibi mamu ya dinga koyi da liman, kada ya dinga riga shi yin wani abu a cikin salla, domin an sanya liman domin ayi koyi da shi, kada ka riga shi, ko ku dinga yi tare. Idan mamu suna da yawa sai su sa Liman a tsakiya Idan mamu mutum daya ne sai ya tsaya a damar liman Idan mace da namiji ne sai namijin ya tsaya a damar liman, ita kuma macan sai ta tsaya a bayan su. Idan mace ce da yaro sai yaron ya tsaya a damar liman ita kuma sai ta tsaya a bayan su. Idan mata da maza ne sai mazan su tsaya a bayan liman matan kuma su tsaya a bayan su. Idan mata ne kawai sai su tsaya a bayan liman, amma su ɗanyi nisa da shi, Idan limamiyar mace ce zata yiwa mata limanci sai ta shiga tsakiyar su, ba zata shiga gaba ba. saboda haka aka ruwaito daga Nana Aisha da Ummu salama idan zasu yiwa mata yan uwansu limanci suna shiga cikin sahun gaba a tsakiya. (Tamamul minna na shaik Albaniy.) 1, Yaro mai hankali da ilmi zai iya limanci saboda hadisin Umru dan Salamah ya jagoranci sallar jam'i tun yana yaro dan shekara bakwai, saboda ya iya Karatun Alkurnani mai girma. Buhari. 2, Makaho zai iya limanci ga masu ido, idan yana da ilmi, kamar yadda Abdullahi dan Ummu maktum ya jagoranci salla a zamanin Annabi saw. Abu Dauda ya ruwaito. 3, Namiji zai iya yiwa mata kawai limanci, saboda Hadisin Zakwan wanda ya ke yiwa Nana Aisha limanci a sallar Tarawihi a watan Ramadan Bukhari 182. 4, Limancin almajiri ga malamin sa, kamar yadda Manzon Allah saw yabi S. Abubakar sallah, ya kuma bi Abdurrahman ɗan Aufu salla. 5, Mai taimama zai iya limantar mai alwala, kamar yadda Amru Dan As ya jagoranci wasu sahabbai lokacin yana da janaba yayi taimama saboda lalurar sanyi. Abu Dauda 6, Matafiyi zai iya jagoranrar mazaunin gida sallah, haka shima mazaunin gida zai iya jagoranrar matafiyi. Shi matafiyi sai ya cika, bayan Anyi sallama sai ya tashi ya ciko sallar sa. Kamar yadda Abdullahi dan Abbas ya yiwa wasu matafiya fatawa, idan za su bi mazauna gida salla dole su cika sallar su. (Tamamul minna) na Shaik Albaniy. 7, Mai ramuwa zai iya koyi da mai salla akan lokaci, hakanan mai salla akan lokaci zai iya koyi da mai ramuwa. Idan sallar tazo ɗaya, a wata mazahabar ko sallar ba ta zo ɗaya zai iya koyi da shi, kowa yana kan niyyar sa. (Duba littafin salatul mumini na Dr. Saidu Alƙahɗaniy domin ƙarin bayani.) 8, Mai yin sallar farilla zai iya koyi da mai nafila, haka mai yin nafila zai iya koyi da mai yin farilla. Kamar yadda yazo a hidisin Muazu Ɗan Jabal, a riwayar Bukhari.yana zuwa masallacin Annabi saw ya bishi sallar insha, sannan ya koma garin su, ya jagorance su, wannan sallar ishar, wato yayi sallar isha sau biyu, ta farko farilla ta biyu nafila. 9, Wasu malamai suna ganin babu laifi mai sallar azahar yayi koyi da mai yin sallar la'asar, haka mai yin salla la'asar zai iya koyi da mai yin azahar, duba littafin Salatul mumini na Dr Saidu Alƙahɗaniy. 10 Idan mutum ya sami liman kafin ya dago daga ruku'u to ya sami wannan rakaa, amma idan sai bayan ya dago ne, to ba zai ƙirga wannan rakaa ba cikin abin da ya samu na sallah. Allah yasa mu dace.
👍 🙏 ❤️ 😂 12

Comments