
Sirrin rike miji
June 20, 2025 at 05:02 PM
Mutane sun fi ba da uzuri da yafiya ga wanda ba su sani ba sama da masoyinsu na gaskiya. To amma me ya sa hakan? Saboda idan masoyinsu ya musu laifi, soyayyar da ke tsakaninsu suke dubawa, sai su riƙa jin kamar wannan laifin cin amanar soyayya ne, kuma ba haka ba ne. Waswasin shaiɗan ne kawai. Wajibi ne mu sani ɗan'adam ajizi ne. Allahn da ya halicce shi ma yana masa laifi, balle kai. Ka riƙa ba wa masoyinka uzuri kamar yadda kake so ya ba ka. ~ Isa Sadi
👍
❤️
❤
👌
😢
🙏
40