Sirrin rike miji
Sirrin rike miji
June 20, 2025 at 05:16 PM
SANARWA GA AL'UMMA Assalamu alaikum wa rahmatullah. Muna matuƙar godiya da jinjina ga dukkan masu bibiyar wannan shafi tare da nuna sha’awa wajen saka talla (advertisement) a ciki. Wannan yana nuna ƙaunar ku da amincewar da kuke da ita, kuma muna godiya ƙwarai da gaske. A halin yanzu dai, bamu yanke shawara na karɓar tallace-tallace ba. Muna nazari da lura da abubuwa da dama kafin mu yanke hukunci. Dalilan da yasa ba mu fara karɓar talla ba sun haɗa da: 1. Kiyaye Sahihanci da Aminci: Akwai tsoron kar talla ta zama hanyar yaudara ko 419 daga wasu mutane da ba a san su ba. Idan hakan ta faru, yana iya shafar sahihanci da amincin wannan shafi. 2. Kiyaye Zargi da Tsegumi: Muna gujewa zargin da mutane za su iya yi kamar "wai sun mayar da shafin kasuwanci", ko "duk wani abu sai da kudi." 3. Fahimtar Juna kan Farashi: A wasu lokuta, idan aka fitar da kudin talla, wasu na ganin ya yi yawa ko kuma ba a yi adalci ba, wanda hakan na iya jawo rashin fahimta tsakaninmu da mabiyanmu. Me ya kamata ku sani? Muna ci gaba da duba yiwuwar bude kofar talla a nan gaba, amma za mu tabbatar da cewa an tsara komai bisa tsari, gaskiya, da amana kafin hakan ya faru. Wannan zai kare shafin da ku masu bibiyarsa. Kuna da ra’ayi? Idan kana/kina da ra’ayi ko buƙata kan a buɗe damar talla nan gaba, za ku iya barin comment a kasa. Zamu karanta kuma mu ɗauki shawarar ku da muhimmanci. Muna godiya da fahimta, goyon baya, da addu'o'in ku. — Gudanarwar Shafin sirrin rike miji
👍 ❤️ 🙏 🫶 34

Comments