Sirrin rike miji
Sirrin rike miji
June 20, 2025 at 07:42 PM
Bayan ya dawo gida tare da abokinsa. Matarsa ta hau shi da faɗa tana cewa, ba na gaya ma kar ka sake zuwa gidan nan da baƙi ba in ba ka sanar da ni ba! Me yasa baka yi mini waya ka tambaye ni zan yi girki ba ko ba zan yi ba? Kuma dama na gaya maka, yau a gidanmu zan ci abincin rana amma saboda taurin kai shi ne kazo da abokinka, toh na ga abin da zaku ci. Kaima ban dafa maka abincin ba balle wani Ƙato y ci. Ni yanzu Ƙanwata nake jira ta gama shiryawa, zamu tafi gidanmu, sauri muke. Bawan Allah ya sallami abokinsa. Shi kuma y dawo gida. Matarsa ta ce, wana kinibibin ne ya sa ka gayyato mini abokinka cikin gidan nan? Ya ce, ki yi haƙuri, kullum in muka haɗu sai ya ce, gaskiya na yi dacen mata mai tarbiya. Sai ya ce, yana so ya auri wannan Ƙanwarki, shi ne na kawo shi don ya ga samfurin tarbiyyar gidan ku a aikace....!!!
😂 👍 😮 ❤️ 😢 🙏 😭 😳 🙆‍♀ 🤣 74

Comments