
Sirrin rike miji
June 20, 2025 at 07:51 PM
Ba kowani aboki ake dauka aboki ko abun yarda ba, dan wani abokin gwargwadon yardan da ka masa gwargwadon cuta da wahalar da kai da zaiyi a rayuwa, dan dama da fuskar masoyi ya ke mu'amalartar ka/ki amma da fuskar maqiyi yake zama da kai dan baya daga cikin masoyan ka/ki na hakika wadda ke son ka da Allah, kuma duk kofar cuta ko tozarci da zai samu zai ma.
Kuyi hattara kuma ku kiyaye irin abokai/qawayen da ku keyi ko sakewa da su, kusan masu son ku na gaskiya da masu son ku dan wata manufa tasu, da masu munafurta da cutar da ku a matsayin masoya ko soyayya.
Ku sani wani maqiyin da fuskar masoyi yake bayyana, ya kuma cutar da kai fiye da cutarwar da maiqin ka a bayyane ba zaima cutar da kai ba. Kuma ku sani masoyi/aboki na iya zama maqiyi kamar yadda maqiyi na iya zama masoyi kuma aboki.
🌺 Fatimah Chikaire
👍
❤️
🙏
❤
😊
😮
20