Sirrin rike miji
Sirrin rike miji
June 20, 2025 at 08:13 PM
🌙 AZKAR NA KWANCIYA BACCI 🌙 📌 1. Ayatul Kursiyyu (Suratul Baqarah: 255): "Allahu la ilaha illa huwa Al-Hayyul-Qayyum…" Fa’ida: Wanda ya karanta wannan ayar kafin kwanciya, Allah zai tura mala’ika ta kiyaye shi har zuwa safiya. (Sahih al-Bukhari) 📌 2. Suratul Ikhlas, Falaq da Nas (3 Quls) Karanta: Qul huwallahu ahad Qul a’udhu birabbil falaq Qul a’udhu birabbin nas Fa’ida: Kariyar Allah daga sharrin dukkan halittu. 📌 3. "Bismika Allahumma amootu wa ahya" Ma’ana: "Da sunanka ya Allah nake mutuwa (barci) kuma da sunanka zan tashi." (Hadisi daga Bukhari da Muslim) 📌 4. La ilaha illa Allahu wahdahu la sharika lahu, lahu-l-mulku wa lahu-l-hamdu wa huwa ‘ala kulli shay’in qadir. Fa’ida: Lada mai yawa da kariya. 📌 5. “Astaghfirullaha alladhi la ilaha illa huwa al-hayyul qayyum wa atubu ilayh.” Karanta sau 3. Fa’ida: Allah zai gafarta masa, ko da zunubansa sun kai girman teku. 📌 6. “Subhanallah” 33× – “Alhamdulillah” 33× – “Allahu Akbar” 34× Fa’ida: Wannan zikiri yana kara karfi da kwanciyar hankali. (Hadisi daga Fatima r.a.) 📌 7. "Allahumma bismika wada’tu janbi, wabika arfa’uhu. In amsakta nafsi faghfir laha, wa in arsaltaha fahfazha bima tahfazu bihi ‘ibadakas-salihin." Ma’ana: Ya Allah da sunanka nake kwantar da kaina, da sunanka zan tashi… Allah ya sa mu dace da bacci mai albarka da mafarki nagari. 🌙✨
🙏 👍 ❤️ 🤲 👏 🤍 😂 👎 💯 113

Comments