DCL Hausa
May 24, 2025 at 05:06 PM
'Yan majalisar dokokin jihar Katsina sun aminta Dikko Radda ya nemi tazarce a zaben 2027
Kazalika, 'yan majalisar dokokin sun kuma yi alkawarin za su saya wa Gwamna Radda "form" din takarar wa'adi na biyu idan har bukatar hakan ta taso.
Kakakin majalisar dokokin Nasiru Yahaya Daura ya ce madadin daukacin 'yan majalisar su 34, sun yanke wannan shawarar ne bayan sun yi la'akari da irin cigaban da Gwamna Radda ke kokarin kawo wa jihar Katsina.