
Intizarul Mahdi
June 6, 2025 at 03:25 AM
🌙 AYYUKAN RANAR ARFAT
🔸 AZUMI – Mustahabbi ne azumtar ranar Arfa ga wanda ba zai yi rauni wurin yin addu'a (addu'o'i) ba.
🔹 WANKA – Kafin zawwali ana so ayi wanka a wannan rana.
🔸 ZIYARA – Wanda ya ziyarci Imam Husain (A.S) a wannan rana ba zai gaza ladan wanda ya samu zuwa Arfa ba.
🔹 DU'A – Ana so ayi addu'ar Imam Husaini (A.S) ta ranar Arfa اَلْحَمْدُ للهِ الَّذى لَيْسَ لِقَضآئِهِ دافِعٌ... da addu'ar اَللّـهُمَّ مَنْ تَعَبَّأَ وَتَهَيَّأ... da kuma Ummu Dawud.
🔸 SALLAH – Sallah Raka'a 2. Raka'ar farko Fatiha 1 - Ƙuliya 1. Raka'a ta biyu Fatiha 1 - Kulhuwa 50 [Sallar Amirul Muminin (A.S)]. Bayan anyi sallama sai ayi Tasbihohin da aka ruwaito a Mafatihul Jinan da Ikbalul A'amal.
🔰 A wannan yini na Arfa an ruwaito muhimman addu'o'i da tasbihohi na neman gafara da tuba ga Allah maɗaukakin sarki. A duba littafan ibada irin su Mafateehul Jinan, Iƙbalul A'amal, da Diya'us Salihin domin ganin cikakkun ayyukan wannan ranar suke.
#arfat #zulhajj #imamhusain #gaza #palestine
📱 https://whatsapp.com/channel/0029VaCAJv2EwEjrsx6pUS20

👍
❤️
7