Intizarul Mahdi
Intizarul Mahdi
June 6, 2025 at 12:14 PM
📜 JAKADUN IMAM HUSAINI (A.S) 🔰 MUSLIM BN AQIL - Shi ne babban jakadan Imam Husaini (A.S), kuma ɗan uwan Imam daga dangin Aqil. Imam ya aike shi zuwa mutanen Kufa domin tabbatar da amincin mutanen Kufa da sahihancin wasikunsu da kuma karɓar mubaya'a daga gare su a makwafinsa. Bayan mutanen Kufa sun yi wa Imam Husain (A.S) mubaya'a ta hannun Muslim, daga baya kuma sai suka juya masa baya da warware ba'arsu ga Imam (A.S) da mi}a kai ga Ibn Ziyad, wanda daga }arshe ya shahadantar da Muslim bn Aqil a ranar Arfa shekara ta 60 bayan Hijara. Sannan yaja gaggan jikinsa a titunan garin Kufa shi da hani mai masaukinsa. 🔰 KAIS BN MUSAHHAR AS-SAIDAWI - Ƙais amintaccen sahabi ne ga Imam Ali (A.S) kuma amintacce ga Imam Husaini (A.S). Mai isar da saƙo ne cike da aminci. Ya kasance mai shiga tsakani Imam Husaini (A.S) da mutanen Kufa da kuma tsakanin Imam da Muslim bn Aqil wajen isar da wasiƙu. Bayan kama Muslim bn Aqil, Imam Husaini (A.S) ya aika ƙais zuwa Kufa da wata wasiƙa. Ibn Ziyad ya kama shi kafin ya isa birnin. An buƙaci ya la'anci Imam Husaini (A.S) da babansa Imam Ali (A.S) a taron jama'a a cikin masallaci. Maimakon haka, Ƙais ya yi yabo ga Imam (A.S) da gargaɗin mutanen kufa cewa Imam Husain (A.S) yana nan isowa gare su, su tashi domin su taimaka masa. An jefo Ƙais daga husumiyyar fadar (kamar yanda aka yi wa Muslim), ya yi shahada a ranar 8 ga watan Muharram, shekara ta 61 AH, kwana biyu kafin shahadar Imam Husain (A.S) a Karbala. 🔰 SULAIMAN BN RAZEEN - Bawan Imam Husaini (A.S) ne, kuma amintaccen jakade. Imam ya aike shi da wasiƙa zuwa ga manyan mutanen Basra yana gayyatar su ga goyon bayansa da dafa masa a wannan juyi nashi - Wannan ya nuna Imam ya yi ƙoƙarin tuntuɓar al'umma a faɗin yankuna daban-daban domin tabbatuwan wannan juyin, ba ga iya mutanen Kufa kaɗai ba. Sulaiman ya isa Basra har ya sadu da wasu daga cikin manyanta. Ibn Jurud ɗaya daga cikin manyan Basra ya kai Sulaiman gaban ibn Ziyad (kafin a naɗa shi gwamnan Kufa) tare da fallasa batun wasiƙar. Ibn Ziyad ya karanta wasiƙar Imam Husain (A.S), ya fusata sannan kuma ya umarci aka kashe Sulaiman nan take. Ya yi shahada a Basra. Shahadarsa ta kasance a lokacin da Imam Husain (A.S) ya nufi zuwa Kufa, wanda shi ne shahidin farko a wannan juyin na Imam (A.S). 🔰 ABDULLAH BN YAKDUR - Mahaifinshi hadimin Manzon Allah (S) ne, mahaifiyarsa kuma tayi hidima a gidan Amirul Miminina (A.S), makusanci ne kuma amintacce. Wasu ruwayoyi sun bayyana cewa shi ne ya ɗauki wasiƙar Imam Husain (A.S) zuwa ga Muslim a Kufa bayan Imam ya jima bai sami wani saƙo daga gare shi ba. Wasu ruwayoyin kuma sun ce an aike shi da wasiƙar zuwa ga mutanen Kufa. An sami ruwayoyi guda biyu da suke cewa: Sojojin ibn Ziyad sun kama shi, kuma Ibn Ziyad (L) ya buƙaci ya la'anci Imam Husain (A.S) da yaƙi sai yasa aka jefo shi daga husumiyyar fada (kamar yanda aka yi wa Muslim da Ƙais). Wannan ya faru a Kufa kafin waƙi'ar Karbala. Wasu ruwayoyi kaɗan sun ce ya isa wurin Imam Husain (A.S) a Karbala kuma ya yi shahada a ranar Ashura tare da sauran sahabban Imam Husain (A.S). #muslimbinaƙil #hanibinurwah #kufawa #juyi #ashura #karbala #gaza #palestinr 📱https://whatsapp.com/channel/0029VaCAJv2EwEjrsx6pUS20
👍 1

Comments