
BBC News Hausa
1.3M subscribers
Verified ChannelAbout BBC News Hausa
Barka da zuwa tashar WhatsApp ta BBC Hausa. Ga bayani kan yadda za mu tsare muhimman bayananku. https://www.bbc.com/hausa/articles/c8xlpd2z0pvo
Similar Channels
Swipe to see more
Posts

Manchester United ta yi tayin fan miliyan 60 kan dan wasan Brentford da Kamaru Bryan Mbeumo, mai shekara 25, bayan da aka ki amincewa da tayin farko da ya kai fam miliyan 55. https://www.bbc.com/hausa/articles/c3wdy4vzyv2o?at_campaign=ws_whatsapp

Wata mummunar gobara da ta tashi a kasuwar sayar da wayoyi da ke birnin Kano ta haifar da ɗimbin asarar dukiya. https://www.bbc.com/hausa/live/cgj8x4j58qet?at_campaign=ws_whatsapp

Trump ya yi wa kasuwancin Elon barazanar cewa gwamnatin tarayya za ta kawo tarnaƙi ga shirin Elon, wanda kuma shi ne ginshinƙin rayuwar shirinsa na sararin samaniya. https://www.bbc.com/hausa/articles/c8e62w38n61o?at_campaign=ws_whatsapp

Yayin da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta cika shekara biyu a kan mulkin Najeriya, wasu makusantan shugaban sun kafe a kan cewa lalle an samu cigaba duk da irin kukan da 'yan kasar ke yi na tsananin rayuwa. https://www.bbc.com/hausa/articles/c5y5z0p5xwdo?at_campaign=ws_whatsapp

Saɓanin shekarun baya, lokacin da matan gida kan shafe tsawon wunin jajibere da daren sallah, suna haƙilon shirya tuwon sallah, a zamanin yau, kuna iya cin girkin sallah, ba tare da hayaƙi ko ƙauri sun bulbule ku ba. https://www.bbc.com/hausa/articles/cn03n6e479vo?at_campaign=ws_whatsapp

Lokacin da Christabel Ngwube wadda 'yar ƙasar Kanada ce 'yar shekara 30 ta samu juna biyu, murna har kunne tana ta yi wa jinjirin fata da adu'a, amma fa daga baya lamarin ya sauya zuwa damuwa. https://www.bbc.com/hausa/articles/c3v56q226w1o?at_campaign=ws_whatsapp

Ɗan takarar shugaban ƙasa a karkarshin jam'iyyar Labour a zaɓen 2023, Peter Obi, ya yi kira ga Musulmin Najeriya da su ci gaba da jajircewa da kuma yin sadaukarwa. https://www.bbc.com/hausa/live/c3rpyzg350et?at_campaign=ws_whatsapp

Ɗan wasan Al-Nassr Cristiano Ronaldo ya ce ba zai buga gasar Club World Cup ba duk da cewa wasu ƙungiyoyin da za su buga gasar sun yi ta zawarcinsa. https://www.bbc.com/hausa/live/cj93rryg1n2t?at_campaign=ws_whatsapp

Sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio, shi ne ya sanar da sanya takunkumin a kan masu shari'a na kotun su hudu a ranar Alhamis. https://www.bbc.com/hausa/articles/ckg471d4zzjo?at_campaign=ws_whatsapp

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya ja hankalin ƴan Najeriya da ka da su yanke ƙauna da gwamnatinsa, inda ya ƙara da cewa abubuwan kyautata rayuwarsu na nan tafe ba da jimawa ba. https://www.bbc.com/hausa/live/cgj8x4j58qet?at_campaign=ws_whatsapp