
VOA Hausa
32.5K subscribers
Verified ChannelSimilar Channels
Swipe to see more
Posts

Amurka ta bayyana cewa ana cigaba da tattaunawa akan gaba ta 2 ta yarjejeniyar tsagaita wutar wacce galibi an amince da ita saidai yanayin sarkakiya da tsawon lokacin aiwatar da ita sun bayyana irin raunin da take da shi. https://shorturl.at/iLrVF

Kotun hukunta laifuffukan musamman da ke Legas ta ki dakatar da sauraron zarge-zargen almundahanar da ake yiwa tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele. https://shorturl.at/urduD

A karshen Janairun 2024 ne wadanan kasashe suka ba da sanarwar ficewa daga kungiyar CEDEAO saboda zargin shugabaninta da yin katsalandan a harkokin cikin gidansu, kuma yunkurin mayar da su cikin kungiyar ya ci tura, to amma sabon matsayin na AES alama ce da ke nuna an fara samun sassaucin ra'ayi. https://shorturl.at/Sz5jf

A yau Laraba, kasar Ukraine ta bayyana cewar hare-haren da Rasha ta kaiwa garuruwan dake kusa da filin daga a gabashin kasar sun hallaka akalla mutane 5 tare da raunata wasu 8 ‘yan sa’o’i bayan wani mummunana harin jirgi maras matuki kusa da birnin Kyiv. https://shorturl.at/btX4B

A jiya Talata Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana shirinsa na sayar da sabbin katunan iznin zama a Amurka masu lakanin “katin zinare” akan kudi dala milyan 5 kowane-kuma manyan attajiran Rasha na iya samun cancantar saye. https://shorturl.at/vmuBp

Hukumar efcc mai yaki da masu yiwa tattalin arzikin Najeriya ta’annati ta gurfanar da karin ‘yan China 16 a gaban babbar kotun tarayyar Najeriya, dake Legas. https://shorturl.at/SBeIL

A jiya Litinin, reshen jihar Kano na jam’iyyar nnpp, ya sanarda dakatar da 4 daga cikin mambobinsa dake majalisun tarayya akan zargin sabawa muradan jam’iyyar https://shorturl.at/EzTBu

Da yammacin jiya Litinin, sun fitar da sanarwar cewa sun nada tsohon shugaban Kenya Uhuru Kenyatta da tsohon Firai Ministan Habasha Hailemariam Desalegn da kuma tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo a matsayin wadanda za su taimaka wajen aiwatar da sabuwar yarjejeniyar sulhu. https://shorturl.at/VQTEY

A ranar Litinin shugaba Donald Trump ya ce, yana gab da cimma kulla yarjejeniya da Ukraine da kuma Rasha domin kawo karshen yakin da ake yi a Ukraine, bayan yini guda da aka kwashe ana ganawa a fadar White House da shugaban Faransa Emmanuel Macron. https://shorturl.at/7cUBW

Shugaban Burtaniya Keir Starmer zai kai wata ziyara mai cike da kasada zuwa fadar White House a Alhamis mai zuwa domin yunkurin gamsar da takwaransa na Amurka Donald Trump ya dauki alkawarin bada kariya ga kasar ukraine a wani bangare na yarjejeniyar tsagaita wuta da rasha. https://shorturl.at/Z8qce